Boko Haram sun datse service din waya a Geidam, jihar Yobe

66

An raba mutane dayawa mazauna garin Geidam da service na waya bayan mayakan Boko Haram sun kone karafunan service na Airtel da MTN a garin.

Geidam ne garin mukaddashin sufeto janar na yansanda, Usman Alkali Baba, kuma nan ne garin tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Geidam.

Maharan sun fara kaddamar da hari a jiya da yamma amma sai suka buya bayan sojin sama sun fara aman wuta.

Daya daga cikin mazauna garin, Ali Maina, yace bayan tafiyar jirgin yakin sojin sama wanda yayi ta shawagi a garin, mayakan sun dawo.

Kazalika, kakakin rundunar yansandan jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da aukuwar harin.

Yace makayan sun yi ta jefar da wasiku dauke da rubutun larabci da Hausa suna neman kafa daular musulunchi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 + eleven =