An shiga rana ta 3 a mamayar Boko Haram a Geidam, jihar Yobe

71

Ba a san inda Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe yake ba tun lokacin da ’yan Boko Haram suka mamaye Geidam a ranar Juma’a.

Babu tabbas ko Buni yana cikin jihar ne ko kuma yana Abuja inda ya fiye zama domin batutuwan da suka shafi jam’iyyar APC mai mulki, wacce yake shugabanta.

Buni ya rike ragamar jam’iyyar APC tun bayan da kotu ta kori Adams Oshiomhole.

Da yawa daga mazauna Geidam sun arced aga garin tun bayan da mayakan Boko Haram da sojoji suka yi musayar wuta a ranar Juma’a.

Bayan hare-hare ta sama daga sojoji, maharan sun ja baya amma sun dawo sa’o’i bayan tafiyar sojojin kuma suna ta yin barna a garin tun daga lokacin.

Kimanin mutane 11 ‘yan gida daya ne aka kashe sakamakon fashewar wani abu da ya faru a gidansu da ke Unguwar Saminaka kusa da sansanin soja a Geidam.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eight + one =