An kashe mutane 45 bayan wasu munanan hare-hare a Zamfara

50

Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun kashe a kalla mutane 45 a yayin da suka kai wani mummunan hari kan kauyuka 6 na jihar Zamfara.

Mutane da dama da suka hada da mata da yara sun yi batan dabo yayin maharan suka kone gidaje, shaguna da gine-gine masu zaman kansu da na jama’a.

Kauyukan sune ‘Yar Doka, Kango, Ruwan Dawa, Madaba, Arzikin Da da kuma Mairairai.

Mazauna kauyukan sun ce da farko wasu mutane dauke da makamai sun yi wa kauyen ‘Yar Doka kawanya a kan babura kuma suka harbe duk wanda suka gani.

An gano cewa daga kauyen ‘Yar Doka, maharan sun zarce zuwa wani kauye da ake kira Kango inda suka harbe akalla mutane 11.

Wani mazaunin kauyen, Halliru Bala, ya ce mahara sun kashe mutane 13 a garin Ruwan Dawa.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Zamfara, SP Muhammad Shehu bai bayar da martani ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × four =