
Adadin wadanda suka rasa rayukansu a kashe-kashen da aka yi a jihar ta Zamfara na karuwa yayin da rahotanni daga kauyuka suka nuna cewa ya zuwa yanzu an binne akalla gawarwaki 90 yayin da mutane da dama suka yi batan dabo bayan rikicin baya-bayannan.
Mutanen da suka rasa muhallinsu, jami’ai da kuma mazauna garuruwan da abin ya shafa ne suka bayar da rahoton hare-haren.
Gwamnatin jihar ta kuma rufe wasu manyan kasuwanni guda hudu domin hana sake afkuwar harin ramuwar gayya daga ‘yan bindiga.
Gwamnatin bata ce uffan ba game da wadanda suka rasa rayukansu yayin da ta yi kira ga jami’an tsaro da su kara kaimi wajen samar da tsaro a kauyukan dake fuskantar barazana.
Mazauna garin Magami sun ce sun binne gawarwaki 60 a safiyar yau, bayan da suka bayar da rahoton gano gawarwakin 53. Sun ce har yanzu mazauna garin da yawa sun bata kuma suna fargabar an kashe su.
Babban Limamin garin, Sanusi Na’ibi, ne ya jagoranci sallar jana’izar.