Tinubu na so a dauki matasa miliyan 50 aikin soja

60

Jigon jam’iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da majalisar kasa su gaggauta kawo karshen matakan tsuke bakin aljihu tare da fito da shirin tallafawa yan kasuwa.

Da yake jawabi a yau a wajen bikin cikarsa shekaru 69 a duniya a Kano, Bola Tinubu yace dole ne kasarnan ta daidaita shirye-shiryenta na tattalin arziki.

Ya kawo misalin tallafin da gwamnatin Amurka ta bawa yan kasuwarta a baya-bayan nan, inda ya nuna bacin ransa akan yadda ake cigaba da samun marasa aikin yi a Najeriya, karkashin wannan gwamnatin.

Ya kara da cewa hakkin gwamnatin tarayya ne ta inganta rayuwar yan Najeriya.

Bola Tinubu ya kuma yi kira ga gwamnati ta dauki karin matasa aiki a bangaren tsaro.

Tinubu ya ce ya kamata a dauki matasa miliyan 50 aikin soja yayin da za a mayar da wasu zuwa aikin gona.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seven − three =