Rashin zaman lafiyar Libya ke jawo shigowar makamai Najeriya – Buhari

49

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce muddin kasar Libya ta cigaba da kasancewa cikin halin ha’ula’i, makamai za su cigaba da kwarara a yankin Sahel na Nahiyar Afirka.

Shugaban ya yi magana ne jiya a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja, yayin karbar bakuncin wakilin musamman na Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya mai barin gado kuma Shugaban Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Yammacin Afirka da yankin Sahel, Mohammed Ibn Chambas.

Shugaba Buhari ya ce Muammar Gadaffi ya rike madafun iko a Libya tsawon shekaru 42 ta hanyar daukar masu tsaro dauke da makamai daga kasashe daban-daban, wadanda daga baya suka tsere da makamansu lokacin da aka kashe Gaddafin.

Shugaba Buhari ya bayyana Chambas, wanda ya kwashe shekaru da dama a Najeriya a mukamai daban-daban, daga ECOWAS zuwa Majalisar Dinkin Duniya, a matsayin dan Najeriya.

Yayi masa fatan alheri a ayyukansa na gaba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 + one =