Babban bankin kasa (CBN) ya bijiro da sabon tsarin haraji kan kwastamomin da ke amfani da lambobi wajen sayen katin waya ko aikawa da kudi daga asusun ajiyar bankinsu.
Bankin ya ce daga jiya Talata, za ake cire harajin naira 6.98 kan kowanne kati da aka saya na layin waya ko aikawa da kudi ta hanyar danna lambobi a waya.
Ya ce sabon tsarin na cikin yarjejeniyar da aka cimma da bankuna da kamfanonin sadarwa bayan wata tattaunawa a ranar Litinin kan bashin naira biliyan 42 da ake bin kamfanonin sadarwa.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa hadin-gwiwa da aka fitar tsakanin babban bankin da kamfanonin sadarwar.
Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dr. Isa Pantami, ya jagoranci zaman ganawa tare da bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudade da kuma masu kamfanonin sadarwar wayar hannu a ranar Litinin.