Buhari ya umarci hukumar shige da fice ta inganta tsaro a iyakokin kasarnan

53

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, yau a Abuja, ya umarci Hukumar Shige da Fice ta Kasa, Immigration, da ta inganta sa ido da tsaro a kan iyakokin kasarnan.

Ya umarci hukumar da ta tabbatar da cewa masu aikata laifuka ba su mayar da Najeriya mafaka ba don aikata laifukansu.

A cewar wata sanarwa daga mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, Shugaban kasar ya ba da wannan umarnin ne a cikin jawabinsa a wajen bikin bude Gini Fasaha na Hukumar Shige da Fice ta Kasa.

An ruwaito shugaban yana kuma umartar dukkan hukumomin tsaro da su habaka ayyukansu na kare rayuka da dukiyoyi, tare da bayar da umarni cewa dole ne a inganta matakin tsaron kasarnan a duniya.

Yayi musu alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ba da goyon bayan da ake bukata don gudanar da ayyukansu.

Ya kuma bukaci Hukumar Shige da Fice ta Kasa da ta hada kai da kungiyoyin tsaro na duniya wajen kiyaye iyakokin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 + 16 =