Yan bindiga sun sace matasa 2 a Mallammadori, jihar Jigawa

144

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace wasu yan uwa biyu a Unguwar Abuja da ke karamar Hukumar Mallammadori a Jihar Jigawa.

Wani mazaunin garin wanda ya zanta da manema labarai ya ce ‘yan bindigar da yawansu ya kai kimanin goma sun mamaye garin na Mallammadori inda suka yi awon gaba da mutanen.

Ya ce ‘yan bindigar sun yi harbin iska, suka mamaye gidan wani Abdullahi Blacki Maidaru, wani dan canjin kudi da ke zaune a Legas suka yi awon gaba da yara biyu a gidansa.

Yace wadanda lamarin ya rutsa da su dukkaninsu matasa ne kuma suna karatu ne a kananan makarantun sakandire a Mallam Madori.

Kakakin ‘yansanda a jihar ta Jigawa, Zubair Aminudeen, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Dutse.

Ya ce ‘yansanda sun samu rahoton kuma za su mai do da cikkaken bayani ga manema labarai.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two + 11 =