Majalisar Dattawa ta karanta wasikar Buhari ta neman tabbatar da hafsoshin soji

47

Majalisar dattijai ta karanta bukatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar mata na tabbatar da sabbin manyan hafsoshin sojin da aka nada.

Bukatar wacce ke kunshe a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 27 ga Janairu, shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ne ya karantata yayin zaman majalisar na yau.

Wadanda aka tura domin tabbatar da su sun hada da Manjo Janar Lucky Eluonye Onyenuchea lrabor a matsayin hafsan tsaro da Manjo Janar Ibrahim Attahiru a matsayin hafsan sojin kasa da Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo a matsayin hafsan sojin ruwa, da Air Vice Marshal Isiaka O. Amao a matsayin hafsan sojin sama.

Shugaba Buhari ya nada sabbin hafsoshin sojin ne bayan cigaba da kururuwar ‘yan Najeriya ke yi na cewa akwai bukatar sabbin hannaye a yakin da ake yi da ta’addanci musamman a yankin Arewa maso Gabas. Sai dai, lauyoyin kare hakkin bil’adama ciki har da Femi Falana sun ce Shugaban kasar ba shi da ikon nada sabbin hafsoshin sojin ba tare da sahalewar majalisun kasa ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × four =