Majalisar Dattawa ta bukaci Buhari ya ayyana dokar tabaci akan tsaro

29

Majalisar dattawa tayi Allah wadai da sace daliban sakandare da yan bindiga suka yi a jihar Neja.

A zaman da ta yi na yau Laraba, majalisar ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaggauta ayyana dokar ta-baci kan matsalar tsaro a Najeriya.

Majalisar tayi kiran ne biyo bayan kudirin da Sanata Sani Musa daga jihar Neja ta gabas ya gabatar dangane da sace dalibai da malaman makaranar kimiyya ta gwamnati dake garin Kankara a jihar Neja.

Sani Musa yace yan bindigar da suka sace su, suna sanye da kakin soji.

Sannan Majalisar ta yi kira ga shugaban kasar ya yi la’akari da kuma aiwatar da shawarwarin da kwamitin wuccin gadi da ta kafa kan ƙalubalen tsaro ya bayar tun Maris din 2020.

A yau ne aka wayi gari da labarin sace dalibai da malaman makarantar sakandiren kimiyya Kagara a jihar Neja kuma har yanzu ba a san adadin yawan wadanda aka sace ba amma makarantar na da dalibai sama da dubu 1.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

thirteen + nineteen =