Gwamnatin Tarayya ta shirya samar da takin zamani buhu miliyan uku a bana

30

Kwamitin shugaban kasa na takin zamani ya tabbatarwa da manoman Najeriya cewa za a samar da takin zamani mai yawa, kimanin buhu miliyan uku a bana.

Shugaban kwamitin kuma gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, ya sanar da haka a jiya a wajen kaddamar da shugabannin jiha da na kananan hukumomin 27 na kungiyar manoma ta Amana, wanda aka yi a Dutse.

Gwamnan yace kwamitin zai yi duk mai yiwuwa wajen samar da takin ga manoma a dukkanin lunguna da sakunan kasarnan kafin damina.

Gwamna Badaru ya tabbatarwa da manoma cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yana shirye wajen basu dukkan hadin kai da goyon baya domin inganta harkokin nomansu a kasarnan. Da yake mayar da martani, shugaban kungiyar manoma ta Amana, Haruna Ahmed Fanbeguwa, yace sun zo jihar ne domin kaddamar da shugabannin kungiyar na jiha da na kananan hukumomi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

10 + five =