Gwamna El-Rufa’i ya bayyana dalilin da yasa hare-hare zai dore a Arewa maso Yamma

72

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi gargadin cewa rashin tsaro zai ci gaba da ta’azzara a shiyyar Arewa maso Yammacin kasarnan muddin jihoshin yankin suka ki hada kan manufofinsu wajen magance hare-hare.

El-Rufai ya yi magana da BBC Hausa a yau biyo bayan kisan gillar da wasu da ake zargin ‘yan fashi suka yi a ranar Asabar a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

‘Yan fashin sun afkawa wani kauye da ke yankin da misalin karfe 5 da rabi na yamma a ranar Asabar kuma sun kashe mazauna kauyen su 18 da kuma yiwa wasu fashi.

Gwamnan yace anyi kokarin hadin gwiwa tsakanin gwamnonin Arewa maso Yamma kan magance matsalar ‘yan ta’adda amma hakan bai yi nasara ba saboda gwamnonin suna yin amfani da hanyoyi daban-daban wajen magance matsalar.

An ruwaito a baya yadda Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, yake cewa sulhun da yayi da ‘yan fashi ya rage kashe-kashen jama’a a jiharsa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four + 15 =