Gwamna Bala Ya Kaddamar Da Shirin Allurar Dabbobi Na Shekarar 2021

25

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya jagoranci kaddamar da shirin allurar dabbobi a sashen kula da lafiyar dabbobi na Galambi.

Lawal Muazu, mai tallafawa Gwamna Bala kan kafafen yada labarai na zamani ya bayyana haka acikin wata sanarwa daya sanyawa hannu jiya Laraba.

Yayin kaddamar da shirin, Gwamna Bala yace allurar riga-kafin dabbobi ita ce hanya mafi alfanu wajen yaKi da cutuka masu yaduwa dake nakasa dabbobin gida. 

Gwamnan ya kara da cewa hukumomin kula da lafiyar dabbobi na jiha sun tallafa gaya wajen mika rahoton bullar cutuka ga asusun kula da lafiyar dabbobi na majalisar dinkin duniya ta hannun ma’aikatar harkar noma da inganta yankunan karkara ta tarayya wanda hakan yasa jihar Bauchi ta samu gudummawar sundukin allurar riga kafin guda dubu shida daga majalisar

Gwamna Bala ya bayya na cewa gwamnatinsa ta samar da kimanin Naira miliyan talatin da biyu da dubu dari da arbain da bakwai da dari biyar don kaddamar da shirin allurar dabbobi, kayan aiki da kuma alawus. 

Gwamnan yace baya ga kudaden shiga da kiwon dabbobin ke samarwa, ana amfana da kayan masarufi da ake samu daga jikin su kana yace gwamnatinsa na sane da kokarin ma’aikatan jinyar dabbobi wajen inganta samar da abinci da kayan kawa. 

A cewar gwamnan, jihar Bauchi na cikin jihohin da suka fi samar da ababen masarufi da kiwon dabbobi kana gwamnatinsa za ta cigaba da hada kai da hukumomin gwamnatin tarayya don fadada shirin a wani matakin inganta tattalin arziki.

Gwamna Bala ya kara da cewa gwamnatinsa ta bada gudummawa me tsoka wajen ilimantar da YaYan makiyaya da kuma zamanantar da noma da kiwo.

Haka kuma Gwamnan ya yabawa kungiyoyin Fulani kan hobbasar su kan inganta zaman lafiya da tsaro a jihar Bauchi kana ya kiraye su, shugabannin kananan hukumomi ashirin, masu rike da masarautun gargajiya, malaman addinai da kuma masana kiwon lafiyar dabbobi da su marawa shirin baya don kai ga nasara. 

Saura da suka yi jawabi sun hada da babban jami’in kiwon lafiyar dabbobi na Kasa Dakta Olaniran Alabi da kuma kwamishinan harkar noma da inganta yankunan karkara Samaila Burga. 

Tun farko yayin taron, kungiyoyin Fulani makiyaya sun yabawa gwamnan kan jawaban sa da ke adawa da tsangwamar Fulani makiyaya da rashin martaba dokoki da ake yi kana suka yi alkawarin cigaba da mara masa baya don tabbatar da nasarar gwamnatin sa. 

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 − six =