Fadar Shugaban Kasa ta bukaci yansanda su wallafa sunayen Fulani Makiyaya dake fuskantar shari’a

55

Fadar Shugaban Kasa ta bukaci hukumar yansanda da ta wallafa sunayen Fulani makiyaya da ke fuskantar shari’a a jihohi daban-daban na kasarnan.

Ta kuma ce shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda shima bafulatani ne, bashi da hannu cikin rikicin makiyayan da ya dabaibaye wasu sassan kasarnan.

Babban mai taimakawa shugaban kasa akan kafafen yada labarai da hulda da jama’a, Garba Shehu, ya sanar da haka a yau lokacin da yake magana ta gidan talabijin na Channels.

Garba Shehu yace abin takaici ne, kalaman batancin da ake yiwa Buhari, kuma ya kara da cewa ana tuhumar batagarin Fulani makiyaya da dama a gaban kotuna.

Garba Shehu yace ubangidansa ba mai san gwaninta bane, inda yace hukumomin tsaro na aiki tukuru domin dakile matsalar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × 2 =