Buhari ya bai wa tsaffin masu yi wa kasa hidima su 110 aikin yi da tallafin karatu

35

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bai wa tsofaffin masu yiwa kasa hidima guda 110 aikin yi tare da tallafin karatu.

Buhari wanda ya bayyana hakan a yau Alhamis yayin wani taron karrama masu yiwa kasa hidimar a fadarsa, ya kuma ba su kyautar kudi.

Matasan na cikin wadanda suka yi wa kasa hidima wato NYSC a shekarar 2018 zuwa 2019 kuma shugaban ya halarci taron ne ta intanet.

Haka nan ya umarci ma’aikatun gwamnati da su tabbatar an bai wa wadanda suka samu kyautar kyautukansu sannan ya yi kira ga matasan da su mayar da hankali wurin ci gaba da halayen da suka sa aka zabe su.

Shugaban ya kuma yi amfani da wannan damar wajen yabawa wadanda suka assasa wannan shiri wanda ya kai shekaru 48, musamman Janar Yakubu Gowon, wanda shima ya halarci bikin ta intanet.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fifteen + seventeen =