Boko Haram sun sake kai hari Geidam a jihar Yobe

161

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne a yau sun kai hari a karamar hukumar Geidam da ke jihar Yobe.

Majiyoyi daga garin na Geidam sun fadawa manema labarai cewa maharan sun mamaye garin ne bayan sallar Magriba.

Harbe-harben da maharan suka yi ya sa mazauna garin da dama firgita inda suka gudu cikin daji yayin da wasu suka buya a gidajensu.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar, Abdulkarim Dungus, ya shaida wa manema labarai cewa ya ji shugaban ofishin ‘yan sanda na Geidam yana harbi da bindiga a lokacin da yake kokarin tuntubarsa.

Geidam na da nisan kilomita 200 daga Damaturu, babban birnin jihar Yobe kuma daya ne daga cikin garuruwan kan iyaka tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar. Hakanan yana da iyaka da jihar Borno daga arewa.

‘Yan kungiyar Boko Haram sun sha kai wa garin hari sau da dama wanda ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nineteen + 2 =