Wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun sace matafiya da yawa a jiya a babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.
Wata majiya ta shaidawa manema labarai a Maiduguri cewa maharan sun yi kwanton baunar ne kan motocin haya da ke bin babbar hanyar a yammacin jiya kuma suka yi awon gaba da fasinjoji da dama.
Daya daga cikin matafiyan, wanda ya tsere, ya fadawa manema labarai cewa maharan sun tsayar da motoci da misalin karfe 1 na dare, inda aka kwashe fasinjojin aka tafi da su zuwa cikin daji.
Ya ce maharan dauke da muggan makamai sun tsaya kan babbar hanyar a Garin-Kuturu kusa da Auno, a karamar hukumar Konduga ta jihar Borno, ‘yan kilomitoci kadan daga Maiduguri, babban birnin jihar.
Ya ce wasu daga cikinsu sun fito daga cikin motocinsu sun gudu zuwa Damaturu, babban birnin jihar Yobe, inda suka fito.
Ba a samu jin ta bakin masu magana da yawun ‘yansanda da sojoji ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
A wani labarin kuma, Kwamandan Boko Haram, Abubakar Shekau ya dauki alhakin harin bam na ranar Talata a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno.
Shekau ya kuma musanta cewa an kwace gonarsa kuma yana alfahari da cewa ya samu nasarar kafa daular musulunchi.
Akalla mutane 12 aka kashe yayin harin wanda aka kai da rokoki.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya ce karin mutane 50 sun samu raunuka.
Bayan harbe-harben, nan da nan sojoji suka aika da manyan motoci masu bindigogi zuwa yankin kuma suka fara shawagi a jiragen sama.