Yan bindiga sun kashe mutane 2 a Kaduna

58

A jiya ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a kauyen Garu da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna inda suka kashe wasu mazauna yankin da aka ambata da suna Aliyu Daiyabu da Safiyanu Muhammad.

Kwamishinan tsaron da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da harin.

Ya ce gwamna Nasir El-Rufai ya aike da ta’aziyya ga iyalan mamatan biyu.

Ya kara da cewa gwamnan ya kuma jajantawa dangin wani mafarauci da aka tsinci gawarsa a karamar hukumar Chikun.

Tun da farko, Aruwan ya ce sojojin Operation Thunder Strike sun cigaba da yin sintiri a yankin Gwagwada dake karamar hukumar Chikun da ta hada babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fourteen + one =