Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta musanta cewa tana shirye-shiryen soke layukan waya dayawa, sandiyyar aikin hada layin waya da number shaidar zama dan kasa (NIN).
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin hukumar, Ikechukwu Adinde.
A cewar sanarwar, ministan sadarwa, Dr. Isa Ali Pantami, ya tabbatar da cewa gwamnati zata cigaba da bibiyar aikin hadawar, da zummar tabbatar da dai-daito.
A baya-bayannan gwamnatin tarayya ta umarci kamfanonin waya da su katse dukkan layukan wayar da ba a hada da number shaidar zama dan kasa ba, bayan wani wa’adi.
Umarnin ya jawo turmutsitsi kasancewar masu amfani da waya a fadin kasarnan, wadanda basu da number shaidar zama dan kasa, sun yi cincirindo domin rijistar samun number kafin wa’adin ya kare.