
Ministan Wuta, Saleh Mamman, ya umarci hukumar kayyade farashin wutar lantarki da ta sanar da dukkan kamfanonin rarraba wutar lantarki da su koma amfani da tsohon farashin wutar lantarki wanda aka yi amfani da shi a watan Disambar 2020.
Babban mai bayar da shawara akan sadarwa ga ministan wuta, Aaron Artimas, ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Yace za’a koma amfani da tsohon farashin wutar lantarkin da nufin dabbaka kawo karshen tattaunawa tare da cibiyoyin kwadago.
Saleh Mamman yace an dauki wannan matakan da nufin magance illar annobar corona, dai-dai lokacin da ake samar da hanyoyin tallafawa yan kasa.
Yace jama’a, na sane da cewa gwamnatin tarayya tare da cibiyoyin kwadago suna tattaunawa akan bangaren wutar lantarki, ta karkashin kwamitin hadin gwiwa.
A cewarsa, an samu cigaba a wadannan tattaunawar, wadanda aka sa ran kammalawa a karshen watan Janairu.