Buhari a karo na biyu ya sake dora alhakin hare-haren yan bindiga akan hakar ma’adanai

74

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu, ya dora alhakin hare-haren ‘yan bindiga a wasu sassan arewa maso yamma da kuma arewa ta tsakiya akan ayyukan hakar ma’adanai a yankin.

Shugaban ya bayyana hakan ne a yammacin jiya a cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun shugaban, Garba Shehu, ya fitar.

Shugaba Buhari ya haramta duk wani aikin hakar ma’adanai a jihar Zamfara a Shekarar 2019 wanda ya danganta da karuwar ayyukan ‘yan ta’addanci.

Daruruwan mutane ne ko dai ‘yan ta’addan suka kashe ko suka sace su a jihohin Zamfara, Katsina, Sokoto, Niger, Kaduna da Nasarawa a ‘yan shekarun da suka gabata.

Akwai rade-radin da ke nuna cewa aikata laifuffukan ya samo asali ne daga hakar gwal da sauran ma’adanai a wadannan jihoshin.

Sanarwar ta Garba Shehu ta ce shugaban ya ba da umarnin sake wani sabon zaman ganawa a yunkurin kawo karshen matsalar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

13 + three =