Yan bindiga sun kai hari kan ayarin motocin Sarkin Kauran Namoda

64

Wasu yan bindiga wanda ba’asan kosu wanene ba, sun kai hari kan Ayarin motocin Sarkin Kauran Namoda Sunusi Muhammad Asha, kan hanyar Zaria zuwa Funtua, Inda suka kashe mutane 8.

Lamarin ya faru ne a jiya Alhamis da daddare, kan hanyar mai nisan Kilomita 70.

An jima ana bada rahoton yin garkuwa da mutane kan hanyar fiye da kwanaki.

Kanin Mahaifin Sarkin Danjeka Kauran Namoda Alhaji Abdulkarim Ahmed Asha, ya fadawa manema labarai cewa, ya samu rahoton cewa an kaiwa sarkin hari ta wayar tarho da misalin karfe 3 na dare.

Kawo yanzu de mutanen da lamarin ya rutsa dasu suna Ofishin yan sanda na karamar hukumar Funtua a jihar Katsina, inda ake cigaba da shirye-shiryen binne gawarwakin mutanen a garin Kauran Namoda.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four + 20 =