Mutane tara mahara suka sace a kauyen Albasun Liman da ke Katsina

49

Wasu da ake zargin mahara ne an bayar da rahoton sun shiga kauyen Albasun Liman dake yankin karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina, inda suka sace mutane 9.

Daga cikin wadanda aka sace akwai wani dalibi dan aji 5 a makarantar sakandiren gwamnati ta Damari, mai suna Umar Mu’awiya, tare da mahaifinsa.

A cewar mazauna kauyen, harin ya auku da misalin karfe 12 da rabi na daren jiya.

Idan za a iya tunawa dai, a ranar Kirsimeti, mutane 8, daga cikinsu akwai matan aure 2 da matasa 6, wadanda aka sace daga wani kauye guda, sun kubuta daga hannun barayin a lokacin da barayin ke bacci.

Da aka nemi jin ta bakinsa, kakakin rundunar yansanda ta jihar Katsina, DSP Gambo Isa, yace za a binciki lamarin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × four =