Boko Haram ta saki bidiyon daliban Kankara da aka sace

93

Kungiyar Boko Haram ta fitar da bidiyon daliban sakandiren Kankara da ta yi ikirarin yin awon gaba da su ranar Juma’ar da ta wuce.

Bidiyon ya nuna daya daga cikin daliban yana rokon gwamnatin tarayya da ta janye sojojin da ta aika domin ceto su.

A cikin bidiyon dalibin ya nemi gwamnati ta rufe dukkan makarantu idan ban da makarantun Islamiyya sannan ta soke duk wata kungiyar kato-da-gora.

Daliban sun kara da cewa an kashe wasu daga cikinsu inda suka roƙi gwamnati ta biya bukatun kungiyar domin ta sake su.

A cikin bidiyon ana iya jin muryar wani mutum wanda da alama dan kungiyar ta Boko Haram ne yana cewa suna nuna wa gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari daliban ne domin ya ga cewa suna cikin koshin lafiya.

A ranar Laraba ne Gwamna Masari yace ya san inda aka boye daliban makarantar sakandaren kimiyya ta maza ta Kankara da aka sace ranar Juma’ar da ta gabata.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × one =