An kashe mutane 7 a wani sabon hari a jihar Kaduna

47

An bayyana cewa kimanin mutane 7 ne ciki harda wani dan shekara 70 da wata Yarinya yar shekara 6 yan bindiga suka kashe a kyauyen Gora Gan dake Karamar hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna.

An gano cewa mutane 4 daga cikin wadanda aka kashe a lokacin da lamarin ya faru yan gida daya ne.

Haka kuma akalla gidaje da Shaguna 13 ne yan bindigar suka kone, bayan da suka kewaye garin da Misalin karfe 8 na Dare.

An kuma samu rahoton mutanen da suka samu raunika a lokacin harin, a cewar sanarwar da gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar.

Kazalika, gwamnatin jihar ta tabbatar da harbe-harben da akayi a kan hanyar Fadan Kagoma zuwa Kwoi ta karamar hukumar Jema’a.

Yan bindigar sun harbi direban wata mota, sai dai gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmed El-rufa’I ya umarci a gudanar da bincike.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × 3 =