Yan bingida sun kai hari kan masallachi a Zamfara, sun kashe mutane 5 tare da sace wasu da dama

63

Wasu yan bindiga a ranar Juma’a sun kai hari kan wani masallachin Juma’a inda suka kashe masallata biyar tare da sace wasu da dama a yankin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Mazauna wajen sun ce lamarin ya auku a kauyen Dutsen Gari dake lardin Kanoma na karamar hukumar ta Maru. Sun ce gomman yan bindiga dauke da muggan makamai sun isa garin akan babura inda suka dinga harbi domin razanarwa tare da kisa.

Sun kara da cewa yan bindigar sun isa garin lokacin da mutanen garin ke halartar sallar Juma’a.

Wani mazauni garin wanda ya nemi a sakaye sunansa yace tunda farko yan bindigar sun yi badda kama a matsayin masallata a masallachin, inda daga baya suka tarwatsa mutane da harbin bindiga kuma suka kashe 5 daga cikinsu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

ten + six =