Wasu mahara yan bindiga sun sace hakimin garin Matseri dake yankin karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara, Alhaji Halilu Matseri tare da yayansa 4.
Sun kuma kashe wani mutum mai suna Maigaiya Matseri, wanda yayi kokarin ceto hakimin.
Sarkin Anka, wanda shine shugaban majalisar Sarakunan Jihar Zamfara, Alhaji Attahiru Ahmed, yace maharan sun isa garin da tsakar daren jiya, inda suka yi awon gaba da hakimin tare sda yayansa.
Wani mazaunin garin, Malam Mohammed Musa, yace maharan sun zo garin akan babura da misalin karfe biyun dare.
Ya kara da cewa da zuwansu, sai suka wuce kai tsaye zuwa gidan hakimin inda suka dauke shi tare da yayansa 4.