An rantsar da shugaba Magafuli na Tanzania bayan zaben da ake takkadama akai

60

An rantsar da Shugaban Kasar Tanzania, John Magafuli, a wa’adi na biyu, biyo bayan nasarar da ya samu a zaben da aka gudanar makon da ya gabata, wanda ake takaddama akai.

Sama da kasashe 12 ne suka tura wakilai zuwa wajen bikin rantsuwar, tare da wakilan kungiyar tarayyar Afirka da na kungiyar cigaban yankin Kudancin Afirka.

Shugaban kasar ya sha rantsuwa a wani filin wasanni a babban birnin kasar, Dodoma, idan jama’a suka yi ta tururuwa da tun da sanyin Safiya.

John Magafuli ya lashe zaben da kashi 84 cikin 100 na kuri’un da aka kada, a zaben da yan adawa suka yi watsi da shi a cewa an tafka magudi.

Babban abokin karawarsa, Tundu Lissu, ya samu kashi 13 cikin 100 na kuri’un.

Hukumar zabe ta musanta cewa an yi magudi a zaben.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

14 + twelve =