
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a dokar kawo sauye-sauye ga aikin ‘yan sanda a kasarnan.
Shugaban Kasar a wata takarda dauke da kwanan watan 16 ga watan Satumbar da muke ciki, ya sanar da majalisa ta hannun akawunta cewa ya sanyawa dokar hannu.
Dokar ta tanadi yadda rundunar ‘yan sandan za ta kasance mai karin nagarta da kuma kyakkyawan tsari a aikinta, bisa manufofi na tabbatar da gaskiya da rikon amana a tafiyar da lamuranta da albarkatunta. Dokar kuma ta tanadi wani tsari na musamman da rundunar za ta rinka samun tallafin kudi kamar yadda wasu manyan cibiyoyin gwamnati suke samu, haka kuma za a kara inganta aikin ta hanyar horo na musamman da za a rinka ba wa jami’an.