Kashe-Kashen Kudancin Kaduna: Gwamna El-Rufa’i ya sassauta dokar hana fita

26

Gwamnatin Jihar Kaduna ta rage dokar hana fita ta awanni 24, da ta kakaba a biyu daga cikin kananan hukumomi hudu a jihar, domin dakile kashe-kashen mutane a bangaren kudancin jihar.

Kamar yadda yazo ta bakin kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Mista Samuel Aruwan, an dauki matakin ne bisa shawarar da hukumomin tsaro suka bayar.

Gwamnatin jihar tunda farko ta rage dokar hana fita a yankunan kananan hukumomin Jema’a da Kaura, a makon da ya gabata, yayin da take bibiyar halin da ake ciki a kananan hukumomin Zango-Kataf da Kauru.

Mista Aruwan, cikin wata sanarwa da SkyDaily ta samu ranar Asabar, yace an rage dokar hana fita ta awanni 24 a kananan hukumomin Zango-Kataf da Kauru, wacce yanzu zata fara aiki daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a kowace rana.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

14 + four =