Gwamna Babagana Zulum na Borno ya tsallake rijiya da baya a harin Boko Haram

119

Gwamnan jihar Barno ya tsallake rijiya da baya daga harin kwantan baunar Boko Haram a hanyar sa ta dawowa Maiduguri daga kananan hukumomin Monguno da Baga, a cewar kakakinsa tare da wasu majiyoyi.

Gwamnan Zulum ya ziyarci kananan hukumomin Monguno da Baga domin rabawa mazauna sansanonin ‘yan gudun hijra kayan abinci.

Mjiyoyi masu karfi da suka tabbatarwa manema labarai aukuwar wannan al’amari sun shaida cewa sojoji da ‘yan sandan dake gadin gwamna Zulum ne suka yi artabu da ‘Yan Boko Haram din har gwamna Zulum ya tsallake wannan hari.

Baya ga gwamna Zulum, wasu ma’aikatan hukumar bada agaji na jihar, sun afkawa wannan tarko na Boko Haram.

Kakakin gwamnan, Isa Gusau, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

11 + 20 =