Buhari ya bukaci shugabannin Afirka da su sake sadaukar da kawunansu a yaki da rashawa

35
Muhammadu Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci shugabannin Afirka da su sake sadaukar da kawunansu domin sake ceto nahiyar daga matsalar rashawa.

A cewar wata sanarwa da kakakin shugaban kasa Femi Adesina ya fitar, shugaban kasa yayi kiran cikin wata wasika da ya rubutawa shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, wanda shine shugaban Tarayyar Afirka, domin bikin ranar yaki da rashawa.

Shugaba Buhari ya kuma bukaci shugabannin Afirka da su tabbatar da gaggauta cimma burin matsayar Afirka akan kwato kadarorin sata.

Shugaban Kasar ya bayyana damuwa dangane da abinda ya kira manyan ayyukan rashawa da ake aiwatarwa a tsakankanin gwamnatocin jihoshi.

Yace irin wannan yanayin ya kawo cikas sosai a harkar gwamnati, wanda ya jawo matsalolin da suka ta’azzara yanayin tatalin arziki da siyasa a Afirka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × 4 =