Ba a iya shiga Kananan Hukumomin Borno bayan hari kan jirgin MDD

64

Akalla kananan hukumomi 9 ne a jihar Borno ba a iya kai kayan agaji saboda dakatar da ayyukan jiragen sama da majalisar dinkin duniya ta yi, biyo bayan harin da yan Boko Haram suka kai kan daya daga cikin jiragen samanta mai saukar ungulu.

Wani babban jami’i a ofishin majalisar dinkin duniya mai kula da ayyukan ceto, ya tabbatar da lamarin.

Kananan hukumomin da ba a iya zuwa a mako guda da ya gabata sun hada da Dikwa da Gamboru-Ngala da Kala Balge, da Damboa da Mobbar da Bama da Gwoza da Kukawa da kuma Monguno.

A ranar 2 ga watan Yunin da ya gabata, mayakan Boko Haram su ka kai hari a Damasak dake yankin karamar hukumar Mobbar, inda suka kashe fararen hula biyu tare da harbo jirgin saman agaji mai saukar ungulu na majalisar dinkin duniya, wanda ya lalace sosai.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × 5 =