Gwamnatin Jihar Kaduna tace babu mahara a tsaunin Zangzang

29

Gwamnatin jihar Kaduna tace sintirin da sojoji suka yi basu gano mahara akan tsaunin Zangzang ba, akasin yadda wasu mazauna jihar suka yi ikirari.

Wasu kungiyoyi a yankin karamar hukumar Kaura ‘yan kwanakin da suka wuce sun yi zargi cikin wata sanarwar da aka yada sosai cewa sama da mahara 600 dauke da makamai ne suke boye kan tsaunin Zangzang.

Gwamnatin jihar Kaduna tace bayan sanarwar, ta gaggauta neman hukumomin tsaro domin daukar matakin gaggawa kan lamarin.

Kwamishina tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya fadi haka cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai.

Aruwan ya kara da cewa gwamnatin jihar kaduna tana nanata roko ga al’umomin da aka bakantawa da kungiyoyi da daidaikun mutane da a koda yaushe suke bin doka saboda a kauracewa kashe-kashe dake cigaba da zagayawa bisa ramuwar gayya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty − 15 =