Corona: Hukumar NCDC ta sanar sabbin mutane 587 da suka kamu ranar Laraba

30

Hukumar dakile bazuwar cututtuka ta kasa NCDC ta sanar da sabbin mutane 587 da suka kamu da cutar corona jiya Laraba, wanda ya kawo adadin wadanda cutar ta kama a kasarnan zuwa dubu 17 da 735.

An samu mutuwar mutane 14 sanadiyyar cutar jiya Laraba, wanda ya kawo yawan wadanda cutar ta kashe a kasarnan zuwa 469.

Sai dai an samu raguwar wadanda suka mutu sanadiyyar cutar jiya Laraba, idan aka kwatanta da mutane 31 da aka sanar da mutuwarsu shekaranjiya Talata.

Hukumar a shafinta na Twitter jiya da dare tace an samu sabbin wadanda suka kamun a jihoshi 18.

Jihoshin sune Lagos, Babban Birnin Tarayya, Rivers, Oyo, Delta, Bayelsa, Plateau, Kaduna, Enugu, Borno, Ogun, Ondo, Kwara, Kano, Gombe, Sokoto da Kebbi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

thirteen + 16 =