Yawan Wadanda Suka Kamu Da Corona a Najeriya Sun Kai 4,151

17

Yawan wadanda suka kamu da cutar corona a Najeriya sun karu zuwa 4,151 bayan cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta sanar da samun sabbin wadanda suka harbu su 239 a jiya Asabar.

Ana cigaba da samun karuwar yawan wadanda suke kamuwa da cutar sosai a kasarnan.

Kididdigar dukkan wadanda suka kamu da cutar kawo yanzu ya nuna cewa an samu mutane 4,151 da suka kamu, tun bayan samun mutum na farko da ya fara kamuwa da cutar a watan Fabrairu. Daga cikin adadin, har yanzu mutane 3,278 suna fama da cutar, yayin da 745 suka warke kuma aka sallame su, inda mutane 128 suka mutu sanadiyyar cutar.

Kididdigar mutane 4,151 da suka kamu ya nuna cewa an samu mutane 1,764 da suka kamu a jihar Lagos, inda jihar Kano ta biyo baya da mutane 576, sai mutane 343 a Babban Birnin Tarayya, da 161 a Bauchi, da 159 a Borno, da 156 a Katsina, da 115 a Ogun, da 110 a Gombe, da 98 a Kaduna, da 96 a Sokoto, da 83 a Jigawa, da 67 a Edo, da 65 a Zamfara, da 64 a Oyo, da 38 a Osun, da 30 a Kwara, da 25 a Nasarawa, da 21 a Rivers, da 18 a Kebbi, da 17 a Delta, da 17 a Plateau, da 17 a Adamawa, da 17 a Akwa Ibom, da 15 a Taraba, da 15 a Ondo, da 13 a Yobe, da 13 a Ekiti, da 10 a Enugu, da 7 a Ebonyi, da 6 a Niger, da 5 a Bayelsa, da 2 a Benue, da 3 a Imo, da 2 a Abia sai 1 a Anambra.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nineteen − eight =