Sojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram 12 tare da ceto mutane 241 a Borno

43

Dakarun Sojin Najeriya na Operation Lafiya Dole sun kashe mayaka dayawa yayin wasu ayyuka a guraren yaki a jihar Borno, a cewar helkwatar tsaro.

Jagoran yada labarai na helkwatar tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya sanar da haka cikin wata sanarwa a Abuja.

Enenche yace mayakan na sansanin soji na musamman a Gamboru, yayin aikin a garin Mudu ranar 24 ga watan Mayu, sun kashe mayakan Boko Haram 12.

Ya kara da cewa sojojijn sun kuma ceto mutane 241 da suke tsare a hannun mayakan, wadanda suka hada da mata 105 da yara 136.

A  cewarsa, an kwato tutocin mayakan Boko Haram 4, da babur 1 da kekune 2 da lasifika 1 da kekunan dinki 2.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × five =