Mayakan Boko Haram Sun Kai Hari Garin Dapchi a Jihar Yobe

38

Mayakan Boko Haram a jiya Litinin da dare sun kai hari garin Dapchi dake jihar Yobe.

Wani mazaunin garin yace an kaddamar da harin da misalin karfe 7 na dare.

An jiyo cewa mayakan sun kone wasu gidaje a garin, yayin da mazauna garin suka arce.

Sojojin Najeriya daga baya sun isa garin inda suka fara musayar wuta da mayakan.

A garin na Dapchi ne ‘yan Boko Haram suka sace dalibai ‘yanmata 117 ‘yan makarantar sakandire a shekarar 2018. Biyar daga cikin daliban sun mutu lokacin da aka sace su, yayin da aka saki sauran gabadaya, in banda Leah Sharibu, wacce aka bayar da rahoton cewa taki amincewa ta bar addininta na Kirista.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × 5 =