Biyo bayan shawarar da kungiyar gwamnonin Arewa ta yanke na mayar da Almajirai zuwa jihoshinsu na asali, akalla Almajirai 904 aka karba a jihar Bauchi.
Kazalika, jumillar Almajirai 819 aka kwashe daga jihar Bauchi zuwa jihoshi daban-daban a fadin yankin Arewacin kasarnan.
Kwamishinan Ilimi na jihar Bauchi, Dr. Aliyu Tilde, wanda yake kula da Almajirai a kwamitin karta kwana na jihar kan cutar corona da zazzabin Lassa, ya sanar da haka lokacin da yake yiwa gwamnan jihar Bala Muhammad bayani a gidan gwamnati.
Yace Almajiran 904 an karbe su daga Kano da Gombe da Filato da Kaduna da Katsina da Nasarawa da Jigawa da Yobe da sauran jihoshin Arewa.
Yace kwamitinsa ya samu nasara wajen karbar Almajiran jihar tare da mayar da wasu zuwa jihoshinsu, in ban da jihar Taraba, wacce ta ki karbar Almajiran da aka mayar mata.