Boko Haram Sun Kashe Sojojin Najeriya Biyu

111

Sojojin Najeriya 2 ne suka mutu a wani kwanton baunar mayakan Boko Haram, a cewar wani jami’i.

An kuma kashe mayakan na Boko Haram su 3 a kwanton baunar, a cewar jami’in.

Jagoran yada labarai na hukumar tsaro, John Enenche, shine ya fadi cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na kasa ya samu.

John Enenche yace dakarun rukuni na 1 na Operation Kantana Jimlan, wadanda ke zagaye a yankin Buni-Yadi zuwa Buni-Gari a jihar Yobe, sun ci karo da bama-bamai dayawa da aka dasa, da kuma kwanton baunar ‘yan Boko Haram.

Yace kwanton baunar ya auku kilomita 8 kafin Buni-Gari a yankin karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe, inda ya jawo mutuwar sojoji 2, yayin da wasu sojoji 3 suka samu raunuka sanadiyyar tashin bama-baman.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 − nine =