Yawan Mutanen Da Cutar Corona Ta Kashe A Fadin Duniya Sun Kai Dubu 200

25

Mace-macen mutane da ake dangantawa da cutar corona ya haura dubu 200 a fadin duniya, yayin da yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da kwayar cutar ake sa ran za su kai miliyan 3 cikin kwanaki kadan masu zuwa, kamar yadda kididdigar kamfanin dillancin labarai na Reuters ya nuna.

Sama da rabin wadanda cutar ta kashe suna kasashen Amurka da Sifinaiya da kuma Italiya.

An bayar da rahoton mutum na farko da cutar ta hallaka a ranar 10 ga watan Janairu a birnin Wuhan na China, kuma an dauki kwanaki 91 kafin yawan wadanda cutar ta kashe su haura dubu 100, daga nan sai aka dauki karin wasu kwanaki 16 kafin yawan mace-macen su kai dubu 200, kamar yadda kididdigar kamfanin dillancin labarai na Reuters ya nuna, ta hanyar amfani da alkaluman gwamnatoci.

Idan aka kwatanta, ana samun kimanin mace-mace dubu 400 kowace shekara sanadiyyar zazzabin cizon sauro, daya daga cikin cututtuka mafiya hadari a duniya.

Amurka ta bayar da rahoton mutuwar mutane sama da dubu 52 da 400 sanadiyyar corona, kawo jiya Asabar da safe, yayin da kasashen Italiya da Sifaniya da Faransa suka bayar da rahoton mutuwar mutane tsakanin dubu 22 zuwa dubu 26 kowannensu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × three =