‘Yan Boko Haram Sun Kashe Mutane 5 A Ayarin Motocin Ali Modu Sheriff

69

Mayakan Boko Haram sun kashe mutane 5 a ayarin motocin tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, akan babban titin Maiduguri zuwa Damaturu.

Wata majiya a hukumomin tsaro tace mayakan sun farmaki ayarin motocin Ali Modu Sheriff a kusa da Auno, mai nisan kilomita kalilan daga Maiduguri.

Majiyar ta sanar da cewa Ali Modu Sheriff yana kan hanyarsa ta zuwa Maiduguri daga Abuja ranar Alhamis da yamma, domin halartar zaman makoki a rana ta 3, na rasuwar mahaifinsa, Galadima Sheriff, wanda ya rasu a makon da ya gabata.

Yace Ali Modu Sheriff yana tafiya cikin ayarin motoci 9.

Majiyar ta kara da cewa mayakan Boko Haram sun bi sahun ayarin motocin a kusa da Auno, inda tace mayakan sunyi musayar wuta da masu kare lafiyar Ali Modu Sheriff da misalin karfe 6:30 na yamma a ranar Alhamis, kuma yayin musayar wutar, an kashe ‘yansanda 2, fararen hula 2 da wani soja guda.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 + 7 =