Shugaba Buhari Zai Yiwa Kasa Jawabi A Yau Da Misalin Karfe 8 Na Dare

61

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yiwa kasa jawabi a yau da misalin karfe 8 na dare.

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya sanar da jawabin da shugaban kasar zai yi, cikin wata sanarwa da ya fitar yau da rana.

Shugaba Buhari ya fara yiwa kasa jawabi akan cutar corona a ranar 29 ga watan Maris lokacin da ya kakaba dokar kulle a babban birnin tarayya da jihoshin Lagos da Ogun, biyo bayan karuwar yawan mutanen da suke kamuwa da cutar a jihoshin.

Shugaban kasar ya sake yiwa kasar jawabi akan cutar ta corona a ranar 13 ga watan Afrilu, inda ya kara wa’adin dokar kullen.

Tun bayan kakaba dokar kullen, an samu mutane 1,273 da suka kamu da cutar ta corona a Najeriya, inda mutane 239 suka warke, yayin da cutar ta kashe mutane 40.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

7 + 14 =