Sojoji Sun Kashe Sama Da ‘Yan Ta’adda 50 A Fadin Kasarnan

43

Helkwatar Tsaro ta kasa ta bayyana cewa gamayyar dakarun sojoji sun kashe sama da ‘yan ta’adda 50 da sauran batagari a fadin yankunan da ake rikici a kasarnan.

Jagoran sashen hulda da jama’a na helkwatar tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya sanar da hakan a Abuja, yayin da yake jawabi ga manema labarai akan ayyukan sojojin a makon da ya gabata.

Yace dakarun operation lafiya dole, wadanda suka hada da sojojin kasa da na sama da na ruwa, sun samu gagarumar nasara a yankunan da ake rikici daban-daban a makon.

Ya bayyana cewa sojojin yayin aragama daban-daban da mayakan Boko Haram, sun dakile hari a kauyen Yamteke cikin yankin karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno, inda suka kashe mayaka 4, tare da kwace bindigogi samfurin AK47 guda 3, da nakiyoyi 2 da kuma wata waya kirar Tecno.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × four =