Shugaba Buhari Ya Bayar Da Umarnin Gaggauta Janye Baragurbin Jami’an Tsaro Daga Kan Iyakokin Kasarnan

54

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin gaggauta janye jami’an tsaro wadanda ke kawo cikas ga rufe iyayokin kasarnan da gwamnatinsa tayi, daga kan iyakokin kasarnan.

Wannan ya biyo bayan gano cewa wasu jami’an tsaro da aka dorawa alhakin kula da iyakokin kasarnan sun saki wasu tankoki 295 makare da man fetur na fasakwauri da aka kama a ranar 17 ga watan Dismanba, ba tare da izini ba.

Fadar shugaban kasa tace sanadiyyar hakan, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa wani kwamitin bincike karkashin jagorancin babban mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na kasa, Manjo Janar Babagana Monguno, mai ritaya, domin gudanar da bincike kan lamarin.

Kwamitin bayan kammala binciken, ya gano cewa jami’an tsaro sun hada kai da wasu mutane wajen sakin tankokin ba tare da izini ba.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar fadar shugaban kasa, wacce kakakin shugaban kasa, Mista Femi Adesina, ya fitar.

Fadar shugaban kasa ba ta ambaci sunan hukumar tsaron da abinda ya shafa ba, haka kuma bata ambaci sunayen mutanen da ake zargin sun aikata aika-aikar ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

thirteen − 4 =