Likitoci Sun Janye Yajin Aiki

34

Kungiyar kwararrun likitoci na Najeriya ta janye yajin aikin da take yi a fadin kasarnan ba tare da bata lokaci ba.

Kungiyar ta fara yajin aikin ranar 25 ga watan Fabrairu, biyo bayan karewar wa’adin kwanaki 21 da ta bawa hukumar kula da jami’o’in kasarnan na ta janye umarnin data bayar cewa sai mai digiri 3 ne zai koyar a makarantun likitoci, matakin da kungiyar tayi watsi da shi.

Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Kenneth Ozoilo, wanda ya sanar da haka yayin ganawa da manema labarai a Jos, yace sun cimma matsayar haka biyo bayan tattaunawar shiga tsakani wacce aka yi tsakanin kungiyar da kwamitocin lafiya da ilimi a majalisar wakilai.

Farfesa Ozolilo ya cigaba da cewa shawarar janye yajin aikin zai bayar da dama domin cigaba da shiga tsakani da tattaunawa domin neman sulhu dangane da matsalar, tare da sauran matsalolin da ke shafar lakcarorin makarantun likitoci a kasarnan.

Kungiyar daga nan sai ta yabawa kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da sauran masu ruwa da tsaki, bisa shiga tsakanin da suka yi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 − five =