Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad Ya Kamu Da Cutar Coronavirus

128

An tabbatar Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya kamu da cutar coronavirus, bayan anyi masa gwaji.

Babban mai taimakawa gwamnan kan kafafen yada labarai, Mukhtar Gidado, ya sanar da haka cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai.

Tunda farko, gwamnan yace ya gana tare da musayar hannu da Mohammed, dan gidan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda aka tabbatar ya kamu da cutar ta Covid-19 a ranar Lahadin da ta gabata.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 + four =