Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace duk da karuwar rashin tsaro da hare-haren Boko Haram, nasarorin da gwamnatinsa ta samu akan kungiyar sun dawo da martabar Najeriya.
Shugaban kasa ya fadi hakan yayin jawabinsa a dandalin Eagle Square dake Abuja, inda ya kaddamar da sabbin jiragen farmaki masu saukar ungulu.
A watan janairun da ya gabata kadai, bayanai daga jaridu da alkaluma sun yi nuni cewa akalla mutane 245 aka kashe a fadin Najeriya.
Haka kuma binciken Expat Insider na shekarar 2019 ya ayyana Najeriya a matsayin kasa ta 3 mafi hadari a duniya sanadiyyar cin hanci da rashawa da kuma rashin tsaro.
Majalisar wakilai ta kasa a makon da ya gabata ta yi Allah wa dai da karuwar tabarbarewar tsaro a kasarnan.
Majalisar tare da majalisar dattawa, sun bukaci Shugaba Buhari da ya sauya shugabannin hukumomin tsaron kasarnan domin magance kashe-kashen mutane a fadin Najeriya, sai dai Shugaba Buhari yayi kunnen uwar shegu.