‘Yansanda Sun Hana Gudanar Da Zaben Kungiyar Miyatti Allah a Jihar Jigawa

117

Rundunar ‘yansanda a Jihar Jigawa ta hana kungiyar fulani makiyaya ta kasa, Miyetti Allah, reshen jihar Jigawa, gudanar da zaben sabbin shugabanni.

Kwamishinan ‘yansanda na jihar, Alhaji Umar Sule Gomna, ya gayyaci shugaba na kasa na kungiyar ta Miyetti Allah, Alhaji Kiruwa Kebbi, wanda yake kula da yadde ake gudanar da zaben, dangane da batun zaben.

An gayyaci shugaban yayinda yake jawabi ga dumbin taron Fulani gabannin gudanar da zaben a dakin taro na Manpower.

Alhaji Kiruwa sai ya katse jawabin nasa inda aka garzaya dashi zuwa helkwatar ‘yansanda bisa rakiyar motocin hilux guda 2 makare da ‘yansanda dauke da makamai.

Wakilinmu wanda yake wajen ya bayar da rahoton cewa watakila masu shirya zaben basu samu izinin gudanar da zaben bad aga ‘yansanda.

Da ake nemi jin ta bakinsa, kakakin rundunar, SP Abdu Jinjiri, ya tabbatar da gayyatar da aka yiwa shugaban kungiyar na kasa, inda ya kara da cewa kungiyar bata sanar da ‘yansanda batun zaben ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one + seven =